Yayinda da yake karanta sanarwar jam'iyyun adawa Ahmadu Bubakar Sise domin bayyana rashin amincewarsu da abun da suka kira yunkurin magudi wanda kuma suka dora alhakinsa akan hukumar zabe CENI da zummzr ba shugaban kasar cika burinsa na samun nasara a zagayen farko.
Alhaji Rabiu Gwanda na jam'iyyar MRND Hankuri ya yi karin basyani akan lamarin.Yace shugaban hukumar zabe ta CENI ya bada izinin a cigaba da zabe na kwana biyu kuma bai fadi garuruwan da za'a yi zabe ba domin doka yini daya ta tanada a dokance. Wannan ma kadai ya bude hanyar yin magudi.
Ya bada misali da Damagaran inda rumfuna 5082 da can sai aka wayi gari aka fitar da 7500.Dole sai sun yi bincike su san yadda aka samo karin rumfuna.
Amma mataimakiyar shugaban hukumar zabe Hajiya Maryama Katanbe ta tabbatar cewa zargin bashi da tushe. Akan rumfunan zabe a Damagaran tace kayan rumfuna 5085 hukumar ta aika Damagaran. Tace sun rantse da Kur'ani basu tare da kowane bangare.
Hukumar tana cigaba da bada sakamakn dake shigowa sannu a hankali.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5