Sokoto na daya daga cikin cibiyoyin da akayi rijistar yan kasar ta Nijar, domin basu damar zabe a inda suke. Wakilin Muryar Amurka, Murtala Faruk, ya nemi jin ta bakin yan Nijar din mazuna Sokoto, inda dayawa suka yi fatan Allah yasa ayi zabe lafiya a tashi lafiya, sun kuma yi addu’ar neman a zabi dan takara na gari da zai yi aikin da ya kamata a kasar.
Yan Nijar mazauna Najeriya sunyi kira ga duk yan takarar da su rungumi kaddara ga duk wanda Allah ya zaba a wannan zaben.
To sai dai kuma wasu yan kasar na ganin cewa akwai wasu sababbin al’amura dake neman kunno kai a wannan zaben wadanda ya wajaba a dauki mataki a kansu. A cewar wani dan Nijar mai suna Adamu Usman, yace ba a san kasar Nijar da futuna ba, sai dai lokacin zabe akan kawo makamai, wanda yayi kira ga ire-iren wadannan mutane da su ji tsoron Allah, domin zasu amsa tambaya.
Wannan ne dai karo na farko da za a baiwa yan Nijar din da ke zaune a makwabtan kasashe damar jefa kuri’a a babban zaben kasar. Wanda yanzu haka yan takara 15 zasu fafata a zagaye na farko a zagaye na farko na zaben Shugaban kasa.
Domin karin bayani.