A yayi da ake shirin gudanar da zaben a kasar jamhuriyar Nijar a gobe lahadi yanzu haka ‘yan Nijar dake Najeriya, sun shirya tsaf domin gudanar da wannan zabe.
A bangare daya dai wasu ‘yan kasar jamhuriyar Nijar da suka sami nasu katin sun bayyana aniyarsu na gudanar da zaben a gobe cikun kwanciyar hankalin da lumana.
Sai dai yayi da wasu ke cewa sun sami katin zaben nasu kuma suna jiran goben ne domin su kada kuri’arsu wasu da wakilin muryar Amurka Babangida Jibril, ya tattauna dasu sunce su kam basu samu katunan su ba a yayin da wasu suka ce sun yi rajista ne a jamhuriyar Nijar domin haka ba zasu iya zabe a Najeriya ba.
Binciken da muryar Amurka ta gudanar ya nuna cewa za’a gudanar da zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisu a cibiyoyi guda uku ne a Lagos, a inda kuma za’a gudanar da irin wannan zabe a wasu jihohi na Najeriya, da suka hada da Lagos, Abuja,da birnin Fatakwal da jihar Katsina.