Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: Mun Kammala Shirye-Shiryen Zabe - CENI


Harabar Humar Zabe Ta Jamhuriyar Nijar CENI
Harabar Humar Zabe Ta Jamhuriyar Nijar CENI

Hukumar zabe ta CENI  a Jamhuriyar Nijar ta ba da tabbacin cewa kayayyin zabe za su isa rumfuna zaben akan kari da sassa dabdan daban na kasar.

Mataimakiyar shugaban hukumar Hajiya Maryama Katambe ce ta bayyana hakan a wata hira da ta yi da wakilin Muryar Amurka, Sule Mumuni Barma.

Ta ba da tabbacin cewa komai na tafiya daidai yayin da ake shirin gudanar da zabukan a gobe Lahadi.

Zabukan da za a yi sun hada da na shugaban kasa da kuma na ‘yan majalisu, zaben da gwamnati mai ci ta ke ikrarin za ta lashe tun a zagayen farko yayin da su ma ‘yan adawa ke cewa su za su samu nasara a zagayen na farko.

Saurari cikakkiyar hirar Hajiya Maryama Katambe da wakilin Muryar Amurka Sule Mumuni Barma domin jin karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG