Jam'iyyar APC Zata Soma Babban Taronta na Kasa Yau Alhamis

APC

Jam'iyyar adawa ta APC zata soma babban taronta na kasa yau Alhamis inda zata fitar da shugabanninta na kasa da kuma tsayar da dan takarar neman kujerar shugaban kasar Najeriya a zaben shekara mai zuwa.
An soma biki a hedkwatar jam'iyyar APC gabanin soma babban taron jam'iyyar yau Alhamis.

A babban taron ake kautata zaton zaben shugabannin jam'iyyar na kasa da kuma tsayar da dan takarar shugaban kasa.

Wasu na son a yi zaben ne ta hanyar jefa kuri'a amma wasu kuma suna son a sasanta musamman wadanda ke da alaka da wanda suke so yayi takarar 2015.

Abubakar Lado Suleja na cikin shugabannin jam'iyyar na riko. Yace idan an samu sasantawa akan mukamin da aka turawa kowane bangare to bukata ta biya. Idan ba'a samu ba to wadanda ke shugabanci na riko yanzu a bari su cigaba koda ma na shekara guda ne.

Dangane da shugabancin jam'iyyar, Lado yace kowa ya tafi yayi nashi tsarin inda za'a tura mukamai. Misali, yace su shugabanni daga arewa sun yi istifakin mayarda shugabancin jam'iyyar zuwa kudu maso yamma. Wato Yarbawa su kawo shugaban jam'iyya. Amma 'yan kwamitin shirya taron kasa sun kai shugabancin jam'iyyar kudu maso kudu. Wannan ya kawo sabani. Yace a duba a gani. Wanda aka amince dashi a yi tafiya dashi a haka.

A zahiri dan takarar shugaban kasa na APC zai fito ne daga arewa, yankin da zallan talakawa ke marawa Janaral Buhari baya. To saidai wasu 'yan jam'iyyar na yada wata manufa daban.

Sabo Imam Gashuwa yace kowanene ya ci zaben fitar da dan takara zasu yi muba'aya dashi. Janaral Buhari shugaban adawa ne wanda talakawa suke goyon bayansa. Amma hakikanin gaskiya manyan mutane suna adawa dashi. Ya ba Janaral Buhari shawara ya jaraba idan 'yan jam'iyya sun zabeshi to shi ke nan. Amma idan ya ga rawar ta canza to cikin matasa ya marawa wani baya ya tsaya takara domin jam'iyyar ta ci zaben shugaban kasa domin kawar da gwamnatin PDP da ta addabi mutanen Najeriya.

Cikin matasan da ake tunane akwai Kwankwaso da Atiku da Nuhu Ribadu. Atiku matashi ne idan an kwatantashi da Janaral Buhari.

Nasiru Gaza yace gaskiya tun da Buhari ya jaraba sau uku bai ci nasara ba to idan an ba Kwankwaso za'a kaiga nasara.

Sanata Haruna Goje na ganin APC ce zata maye gurbin PDP a zaben 2015 domin watsar da PDP da 'yan siyasar gaskiya suka yi. Yace a kowane yankin kasar sun samu mutane isassu fiye da yadda suke tsammani ma. Barazana da bada tsoro kada su hana mutum komawa jam'iyyar APC saboda dimokradiya ake yi. Ya roki jama'a a yi siyasa cikin kwanciyar hankali.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Jam'iyyar APC Zata Soma Babban Taronta Na Kasa Yau Alhamis - 3'10"