Wannan aikin ya shafi rukunonin jihohi goma ne na farko a cikin jihohi 36 da Abuja da za'a fara bada katin.Mataimakin daraktan hulda da jama'a na hukumar zaben Nick Dazan na zaga johohin da suka hada da Taraba, Gombe , Zamfara, Kebbi, Benue, Kogi, Abia, Enugu, Akwa Ibom da Bayelsa. Dazan yace sun ware naurorin da suka yi anfani da su a zaben 2011.
Hukumar ta gyara naurorin 2011 domin ta rage kashe kudi. A wannan rukunin na daya Dazan yace ba'a sami korafe-korafe ba akan cewa naurorin basa aiki. Saidai a jihar Gombe inda bikin Mauludi ya zo daidai da ranar da suka soma yin ragista.
Bisa ga sheilar da hukumar ta INEC tayi duk wanda bai samu katin zabe na dindindin ba yana iya zuwa ofishin hukumar a kowace karamar hukuma ya mika katin wucin gadi a bashi na dindindin.
Sanata Haruna Goje na cikin wadanda suka kokawa shugaban hukumar zaben domin a samu gyara. Yace akwai mazabu da yawa wadanda gaba daya sunayensu basu fito ba musamman a kananan hukumomin Gombe da Yelmetu da Akko. Yace na Akko ya fi muni domin kusan kashi sittin cikin dari na mazabu basu samu yin ragistan ba saboda wasu dalilai da basu gane ba. Ya kira duk wadanda basu samu yin ragista ba da su fito kowace jam'iyya suke. Duk wanda bai fito ba yayi ragistan ba to baya cikin zaben shekara mai zuwa.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.