WASHINGTON, DC —
A cewar masu neman tsayar da gwamna Rabiu Kwankwaso suna ganin shekaru sun kama Janaral Buhari kuma yakamata yayi ritaya daga siyasa, ya koma gefe ya huta.
Amma magoya bayan Janaral Buhari sun bara akan batun. Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda na cikin wadanda suka bara da yunkurin dakatar da Buhari. Yace Janaral Muhammed Buhari shi ne APC. Yace yau idan babu Janaral Buhari kowa sai kwabarsa ta cika da ruwa. Wadanda suke son su tsayar da Rabiu Kwankwaso ra'ayinsu ne amma basu ji ra'ayin 'yan Najeriya ba. Yace nagartar Buhari kamar nisan sama da kasa ne da nagartar Kwankwaso. Yace kada a yaudari kowa. Idan aka ce yau ga Janaral Buhari babu wanda zai yi maganar Rabiu Kwankwaso.
To saidai magoya bayan Rabiu Kwankwaso irin su Salisu Ayo Gauna cewa suke idan shugabanni da shi Buhari suka zauna suka yadda a tsayar da Rabiu Kwankwaso zasu yi farin ciki.
Da aka tuntubi Bola Tinubu tsohon gwamnan Legas kuma shugaban APC yace a bari har sai lokacin yayi. Yace ba siyasa suka zo yi ba. Ta'aziya suka zo yi.
Alhaji Musa Gwadabe tsohon ministan kwadago yace babu wanda ya isa ya hana a yi zabe idan an zo fitar da dan takara amma sai dai idan Buhari yace baya so.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.