WASHINGTON, DC —
Batun zaben shekara mai zuwa yasa mutanen arewa da kudancin Filato sun soma kai ruwa rana akan bangaren da ya kamata gwamna ya fito a zaben 2015.
'Yan siyasan bangarorin biyu sun fara musayan yawu akan wanda zai gaji gwamna Jonah Jang wanda daga arewacin jihar ya fito.Lamarin yasa a jihar har yanzu babu wanda ya fito gadandagan yace shi zai tsaya zabe tamkar basu da alkibla ko kuma suna cikin duhu.
A wani taron manema labarai da kungiyar dake fafitikar a bar 'yan arewa su cigaba da mulki a zaben shekarar 2015 shugaban kungiyar kuma tsohon shugaban karamar hukumar Jos ta gabas Daniel Izang ya zargi 'yan kudancin Filato da hanasu shiga zabe. Yace tun da aka kafa Filato ba'a taba zama an ce za'a yi mulkin karba-karba ba. Lokacin da Jonah Jang yake neman zabe Sanata Victor Lar daga kudanci yayi takara dashi. Ita ma mataimakiyarsa daga kudanci tana kan mukaminta ta fita ta nemi zama gwamna. Dan arewa dai ya gaji Jonah Jang.
Amma su kuma 'yan kudancin jihar gani suke tun da Jonah Jang yayi shekaru takwas to makaya yayi wani daga kudanci ya gajeshi. Tshohon kakakin majalisar dokokin jihar Mr. George Daika yace su 'yan kudancin jihar basu taba yin gwamna a Filato ba.Marigayi Solomon Lar da Fidelis Tapgun da suka fito daga kudanci basu gama wa'adin mulkinsu ba. Ban da haka lokacin wadan nan mutanen lokacin da jihohin Nasarawa da Binuwai suna tare da Filato ne. Da aka soma jihar Filato Dariye daga tsakiyar jihar yayi shekara takwas kodayake Botman daga arewea ya dan rike na watanni shida. Bayan Dariye ne arewa ta samu, wato shi Jonah Jang ke nan. Yakamata ace kujerar gwamna ta tafi kudancin jihar a zabe mai zuwa.
Ga cikakken rahoto daga Zainab Babaji.