A wata dambarwar siyasa da ta kunno kai a jihar Nasarawa, jam'iyyar APC ta kori mataimakin gwamnan jihar
WASHINGTON, DC —
Wata dambarwar siyasa ta kunno kai tsakanin Damishi Luka Barau mataimakin gwamnan jihar Nasarawa da jam'iyyarsa ta APC.
Dambarwar siyasar ta kaiga korar mataimakin gwamnan daga jam'iyyar APC yayin da shi ma ya canza sheka zuwa jam'iyyar PDP.
A taron manema labarai da mataimakin gwamnan ya kira a garin Lafiya ya bayyana cewa rashin gamsuwa da akidar jam'iyyar APC da nuna wariya da a keyi masa su ka sa ya canza sheka zuwa PDP. Yace na farko shi bai shiga APC ba sai ya ji an cireshi daga jam'iyyar to ashe ko basu da akida.
Dangane da tafiyar da mulkin jihar mataimakin gwamnan yace babu abun da ya shafi siyasa da mulki. Yace gwamnan jihar gwamnanshi ne shi kuma shi ne mataimakinsa. Wannan ba zai kawo damuwa ba. Yayi kwatanci da majalisar dokokin jihar inda jam'iyyar PDP ke da rinjaye kuma ana cigaba da mulki ba tare da wata tangarda ba. Kowace jam'iyya suke an zabesu ne su yiwa jama'a aiki. Yace yana shirye ya baiwa gwamnan goyon baya dari bisa dari domin su ci nasara.
Tun farko jam'iyyar APC ta zargi mataimakin gwamnan da yin wasu kalamai da tace sun sabawa akidarta lamarin da ya kaita korarsa. Shugaban jam'iyyar APC na jihar Stanley Buba yace kwanan baya jam'iyya ta umurci 'yan majalisarta dake majalisun tarayya su yi takatsantsan da duk abun da shugaban kasa zai kawo domin ganin irin abun dake faruwa a jihar Rivers. Shi kuma mataimakin gwamnan Nasarawa ya fito karara yace shawarar jam'iyyar ba ta kan ka'ida. Wannan furucin nasa ya sabama dokar jam'iyyar. Dokar jam'iyyar APC bata yadda wani danta yayi wata magana ba ba tare da samun izin yin hakan ba. Stanley Buba yace duk wanda ya san tarihin mataimakin gwamnan babu wata jam'iyya da bai shiga ba kama daga PDP inda ya koma yanzu. Canza shekarsa bai ba APC mamaki ba domin abun da ya saba yi ne.
To saidai lokacin da ake cikin wannan dambarwar tawagar sakarunan Mada yankin da mataimakin ya fito ta kawo ziyara wurin gwamnan jihar. Chum Mada Samson Gamyare yace su fatansu hankalinsu ya dawo wuri daya domin su samu cigaba. Yace babu ruwansu da takaddamar dake cikin 'yan siyasa. Su iyaye ne sai dai su ja masu kunne kada su tayar masu da rigima. Abun da ya kawo su wurin gwamna shi ne shirin gina sabon asibiti a Akwanga da kasuwa da filin kwallon kafa da wasu ayyukan. Yace sun zo ne su godewa gwamnan da sake jaddada goyon bayansu gareshi.
Ga rahoton Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5