Alhaji Tijjani Musa Tumsa sakataren jam'iyyar APC ya kara haske kan taron da jamiyyar zata yi yayin da yake zantawa da wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda a Abuja. Yace makasudin taron shi ne su bayyanawa alummar Najeriya manufofin jam'iyyarsu. Zasu bayyanawa kasa irin nasu shirye-shiryen idan Allah Ya sa suka kafa gwamnati shekarar 2015.
Taron zai fadakar da duka al'ummar Najeriya kan yadda APC zata tafiyar da kasa wanda zai sha banban da yadda PDP keyi yanzu da ya kusa kai kasar halaka. Dangane da rikicin dake faruwa a cikin jam'iyyar kan shugabanci da kuma taron kasa Alhaji Tumsa yace basu da wani rikici na zaben shugabannin jam'iyyarsu. Nan ba da dadewa ba zasu yi taron kasa su fitarda shugabanni.
Bayan taron da zasu yi gobe ne zasu fitarda kadan cikin abubuwan da zasu saka cikin tsarin yadda zasu gudanar da mulkin kasar idan har Allah Ya basu madafin iko a shekara mai zuwa. Bayan haka zasu yi taron kasa baki daya domin zaban shugabannin jam'iyyar na kasa baki daya.
Taron na gobe sun gayyaci duk manyan mutane da suka taimaka aka haifi APC da abokananta da kungiyoyin cigaban al'umma masu zaman kansu na cikin gida da waje. Sun gayyaci Najeriya gaba dayanta.
Dangane da taron kasa da za'a yi jam'iyyar APC na ganin lokacin irin wannan taron bai yi ba. Saboda haka ba zasu halarci taron ba a jam'iyyance. Yace amma a nasu taron suna son su cigaba da yadda Najriya take su kara mata mahimmanci, su fuskanci abubuwan da kasashen da suka cigaba suka fuskanta, su fuskanci harakar tsaro da duk abubuwan da zasu kyautatawa rayuwar al'ummar kasar.
Ga firarsu da Medina Dauda.