Sarkin Akko ya yi jawabin ne a wurin taron zaman lafiya da masautarsa kan shirya lokaci lokaci domin karfafa zamantakewa a masarautar tasa. Alhaji Atiku sarkin Akkon yace a masarautarsa sukan zauna su duba yadda al'ummomi ke zama da cudanya da juna. Yace sukan tattauna kan yadda kabilu daban daban da addinai daban daban da al'adu da matasa duk za'a yi tafiya tare cikin lumana. Burinsa shi ne a yi yunkuri wajen daidaitawa a kan kowane irin fito na fito cikin al'umma. Yace sun yi dace domin gwamnansu mai yin ayyukan kwarai ne na zahiri da kuma son hada kawunan jama'a. Sabili da haka idan ba an zauna lafiya ba gwamnati ba zata iya yin manya-manyan ayyuka ma jama'a ba. Yace a gaskiya sun anfana da zaman lafiya da suka samu a wannan lokacin.
Alhaji Ahmed Shehu Kumo shugaban kungiyar cigaban masarautar Akko yace sun kafa kungiyar ne domin cigaban masarautar kuma suna aiwatar da wasu abubuwa kamar maganar ilimi. Kungiyar tana karfafa matasa. Ban da haka 'yaransu da suka gama karatun jami'a da makamantansu suna bin gwamnati domin a basu aiki domin ya rage masu zaman banza kana su raya kansu da kasar. Kungiyar tana sa ido a kan abubuwan da gwamnati keyi ko kuma wasu ma masu zaman kansu. Duk abun da zai cutar da jama'a zasu je su yi bayani.
Shi ma Alhaji Babangida Danja Kumo yace a yankinsu akwai ayyuka da yawa da gwamnati ta yi masu kuma mutane sun fahimta cewa domin anfaninsu aka yi su. Mutane kuma sun himmatu cewa idan suka yi wasa suka lalace to zasu dade basu samu irin wadannan ayyukan ba.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammed