Jam'iyyar Adawa Ta NPP A Ghana Za Ta Kaddamar Da Kundin Manufofinta

Wani magoyin bayan jam'iyyar adawa ta NPP a Ghana

Babban jam’iyyar adawa ta New Patriotic Party ko NPP ta kasar Ghana tace zata kaddamar da kundin manufofin jam'iyyar a ranar 18 ga watan Oktoba, inda zata bayyana matakan da zata dauka na gyaran kasa da kuma kau da talauci da wahalhalu da yan kasar ke fama da shi.

A wata hira da yayi da Muryar Amurka, darektan sadarwan NPP Nana Akomea yace akwai muhimmanci yan Ghana su kimanta kokarin shugaban kasa mai ci yanzu John Dramani Mahama da irin alkawura da yayi masu yawa a shekarun baya.

Maganar ta Mr. Akomea ta biyo bayanda shugaba Mahama ya bayyana wasu daga cikin manufofin dake kunshe a kundin jami’iyarsa ta National Democratic Congress ko NDC mai mulki shekaranjiya Talata.

Alkaura da shugaba Mahama ya yi idan an zabeshi, sun hada da shirin ba kowane dalibi na’urar komputa, da kara yawan jihohin kasar daga 10 zuwa 15, sai kuma biyan kudin jarrabawa na kowane dalibin da zai dauki jarrabawan makarantar sakandare. Shugaba Mahama ya kuma yi alkawarin gina sabbin filayen wassani guda biyar idan an sake zabansa.

Sai dai kuma Nana Akomea yace ba’a taba baiwa abokan adawar shugaban kasar damar su jagoranci kasar, yace wannan ne babban dalilin da yasa masu kada kuri’ar su yi zurfin tunani a kan wa’yannan alkauran da da jami’iyar NDC mai mulki ke yi.

Jami’iyar NPP tace NDC tana wa’yannan alkaura ne saboda ta ja ra’ayin masu zabe su jefa musu kuri’a a zaben shugaban da na ‘yan majalisu da za’a yi a can Ghana a ranar 7 ga watan Desimba.