A cibiyar al'adu ta ofishin jakadancin Amurka a Nijar aka gudanar da gidauniyar a karkashin shugabancin jakadiyar Amurka dake kasar wato Jakadiya Redeck.
Mata da suka mallaki kamfanonin kansu suka kafa gidauniyar da zummartaimakawa wadanda rikicin Boko Haram ya daidaita a yankin Diffa cikin Nijar din.
Maryama Dauda babbar sakatariyar kungiyar tace sutura babban abun ne shi ya sa suka maida hankali akan tara sutura domin su raba. Tace duk wanda bashi da sutura bashi da mutunci. Dalili ke nan da suka kira bangarori daban daban da kungiyoyi su tattara tufafi. Ko riga daya mutum ya kawo zata yiwa wani anfani a yankin Diffa.
Ministan al'umma Madam Kafaratu Jaku ta kira al'ummar Nijar su kawo kowane irin kayan sawa ne, tsoffi da sabbi duka suna bukata.Suna bukatan kayan yara ma.
'Yan gudun hijira a yankin Diffa na cikin wani hali na tsaka mai wuya, inji Madam Jibo Halima Hassan wadda ita ma 'yar yankin Diffa ce. Tace mata sun haihu a hanya lokacin da suke gudu. Mutane sun taka wajen kilomita saba'in ba takalma a kafafuwansu