Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zaben Ghana Ta Zafga Kudaden Shiga Takara


Tambarin Hukumar Zaben Ghana
Tambarin Hukumar Zaben Ghana

Masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar Ghana, sunce kudade da hukumar zabe ta nemi masu takarar shugaban kasa da na ‘yan Majalisu su biya a zabe mai zuwa sunyi tsada.

Hukumar zaben dai ta bukaci masu takarar shugaban kasa da su biyu kudin Ghana Cedi 50,000 sai kuma ‘yan Majalisu su kuma su biya Cedi 10,000. Hakan yasa ake ta korafi nan da can a cikin kasar.

Sakamakon haka hukumar zaben tace zata koma ta yi nazari akan wannan batu, inda zata duba ta ga ko zata iya rage yawan kudaden kamar yadda shugaban sashen sadarwa na hukumar zaben Eric Dzakpasu ya nuna.

Alhaji Yusif Jajah, mai yiwa jam’iyyar NDC mai mulki takara, yace idan har an rage kudin tabbas suna so idan kuma ba a rage ba duk da haka zasu biya. Shi kuma Alhaji Issaka Saeed, jami’i a sashen sadarwa na babbar jam’iyyar adawa ta NPP a jihar Ankara, wanda yace su dai ‘yan adawa kudin da aka zabga yayi yawa, kuma suna sauraren su ga abin da hukumar zabe zata fito da shi.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG