Shakaru da dama masu sana'ar fatu a jamhuriyar Nijar ke kwasan garabasa musamman lokacin sallar layya to amma a wannan shekarar lamarin ya zo masu a karkace ba yadda suka saba ba sakamakon faduwar darajar Nera.
Alhaji Bodari daya daga cikin masu sana'ar fatu yace da su kan sayar da awon fata dari biyar ko jaka biyu. Suna kai fatun ne Najeriya to amma yanzu Najeriya bata haraka saboda farashin fatun ya fadi a Najeriya sakamakon rashin kudi. Wannan lamarin ya sa farashinta ma a Nijar dole ya fadi.
Faduwar darajar Nera ya shafi 'yan kasuwar Nijar da dama domin ta dagula masu harkokin kasuwanci..Wani dan kasuwar Nijar yace duk abun da 'yan Najeriya suka kai Nijar zasu ci riba amma idan su sun kai kayansu Najeriya faduwa yake yi.
Alhaji Yakubu Dan Maradi shugaban kungiyar 'yan kasuwan Nijar yace Najeriya ce take atishawa amma su ne suke kuka saboda karyewar darajar Nera ya sa kasuwanci baya yiwuwa a Nijar. Yace kasar gaba daya take ji a jikinta illar faduwar darajar Nera a Najeriya.
An bukaci gwamnatin kasar Nijar ta kafa wata ma'aikatar da zata sarafa fatu domin su dinga kaita kasashen waje suna sayarwa.
Ga rahoton Yusuf Abdullahi da karin bayani.