A jiya Litinin ne Shugabanni biyu na kungiyar kare hakkin bil adaman da suka hada da jarumin dan wasan siniman nan na Amurka, George George Clooney da wani mai fafutukar kare hakkin jama’a, John Prendergast, suka bayyana sakamakon nazarinsu a wurin taron manema labarai a cibiyar yan jarida ta kasa a Washington.
Rahoton da kungiyar tasu mai suna The Sentry ta tsara ya zargi shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar da wasu manyan hafsoshin sojan kasar da kwasar ganimar miliyoyin dololi daga bitalmalin kasar tun shekarar 2005, lokacin da aka kulla yarjejeniyar zaman lafiya wacce ta kai ga samun yancin yankin kudu daga Sudan.
Pandergast ya roki Amurka da sauran gwamnatocin kasashen duniya da su dauki matakan tabattar da wannan dukiyar haramun da aka sato bata ratsa ta cikin cibiyoyin kudade na duniya ba.
Rahoton kungiyar mai shafi 65 yace yakin Sudan ta Kudu da aka share kusan shekaru uku ana tafkawa, ya ta’azzara ne sakamakon rigingimu a kan dukiyar kasa da bangarorin ke neman su koma karkashin rikonsu.