Wannan aika aika cikin sauki, hade da makudan kudaden fansa da masu garkuwa da mutane ke samu kafin su sako mutanen da su ka sace, alama ce mai nuni da cewa hakan zai kara yin muni.
Gazawar jami’an tsaro da shugabannin gwamnati wadanda ke da alhakin kare lafiyar ‘yan kasa wajen daukar matakan dakile wannan dabi’a, shi ma wani bala'i ne da ake iya ci gaba da fuskanta idan ba a magance shi yadda ya kamata ba.
A tattaunawarsa da Shugaban Sashen Hausa, Aliyu Mustapha Sokoto, kan halin da ake ciki game da batun sace dalibai akai-akai a makarantu a yankin arewacin Najeriya, da sauran batutuwan tsaro, ministan tsaro Alh. Abubakar Badaru, ya ce nan ba da dadewa ba gwamnati za ta kawar da ‘yan bindiga, da ‘yan fashi, tare da alkawarin dawo da daliban da ‘yan bindiga suka sace kwanan nan daga wata makaranta da ke Kuriga ta karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
Saurari cikakkiyar hirar:
Your browser doesn’t support HTML5