Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Na Neman Daliban Da Aka Yi Garkuwa Da Su


Sojoji Najeriya
Sojoji Najeriya

Sojojin Najeriya sun fita farautar ‘yan bindigar da suka yi awon gaba da daliban makaranta kusan 300 a jihar Kaduna a makon da ya gabata, kamar yadda wata majiyar tsaro ta bayyana, yayin da iyayen da ke cikin rudani ke bibiyar lokacin da za su sake sa ido ga 'ya'yansu.

Majiyar ta ce runduna ta daya da ke Kaduna ce ke jagorantar aikin kuma nan ba da jimawa ba “za su gano ‘yan bindigar.”

Majiyar ta kara da cewa sojojin sun samu goyon bayan jami’an ‘yan sanda, hukumar leken asiri da na sama, da kuma hukumar ‘yan banga ta jihar Kaduna, kungiyar ‘yan banga da ta san yanayin yankin.

“Hukumomin tsaro da gwamnatin jihar suna aiki tukuru domin tabbatar da ‘yancin duk daliban da aka sace, muna kuma samun ci gaba,” in ji Muhammad Shehu Lawal, mai magana da yawun gwamnan jihar Kaduna, ba tare da bayar da cikakken bayani ba.

An toshe hanyar da ta hada dajin Birnin-Gwari da jihar Zamfara.”
An toshe hanyar da ta hada dajin Birnin-Gwari da jihar Zamfara.”

Sojojin Najeriya ba su amsa bukatar jin ta bakinsu ba.

Satar jama’a da aka yi a ranar Alhamis din da ta gabata, ya girgiza garin Kuriga mai nisan kilomita 90 daga babban birnin jihar Kaduna, inda iyaye ke jiran amsa daga hukumomi.

Kungiyar Boko Haram ce ta fara garkuwa da mutane a makarantu a Najeriya, inda ta sace dalibai sama da 200 a makarantar ‘yan mata da ke garin Chibok a jihar Borno shekaru goma da suka gabata. Har wa yau ba su sake wasu daga cikin ‘yan matan ba.

Sai dai tun daga lokacin ne kungiyoyin masu aikata laifuka suka koyi amfani da wannan dabara na neman biyan kudin fansa, inda da alama hukumomi ba su da ikon hana su.

Satar mutane dai na raba iyalai da al’ummomin da sai sun hada dan abin da suke da shi don biyan kudin fansa, wanda galibi kan tilasta wa iyaye sayar da dukiyoyin da suka fi daraja kamar filaye da shanu da hatsi don a sako ‘ya’yansu.

Bala Ibrahim, wanda dansa na cikin yaran da suka bace, ya ce babu wani karin bayani daga hukumomin yankin kan inda daliban suke ba. Ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho cewa, “Abin da kawai muka sani da ya faru tun bayan garkuwar shi ne an tura sojoji tare da toshe duk wata hanya da ta hada dajin Birnin-Gwari da jihar Zamfara.

"Sojoji suna cikin daji suna bibiyar masu garkuwar."

A cewar wata cibiyar tuntuba ta SBM Intelligence da ke Legas mutane 4,500 ne aka yi garkuwa da su a duk fadin Najeriya tun bayan hawan Tinubu mulki a watan Mayun da ya gabata.

Masu sharhi kan harkokin tsaro sun ce shugaban da ya yi alkawarin magance matsalar rashin tsaro, har yanzu bai fito ya fayyace ta yadda zai tabbatar da tsaro a Najeriya ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG