ABUJA, NIGERIA - Ko a baya bayannan sai da mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan sha’anin tsaro, Manjo Janar Babana Monguno ya bayyana zaben a matsayin wanda ke cike da sarkakkiya fiye da wanda aka yi na shugaban kasa.
Akwai dai jihohin da masu sharhi ke fargabar barkewar mummunar rikici, kamar Kano, Bauchi, Sokoto, Kebbi, Gombe, Zamfara, Kaduna, Lagos da sauransu.
Masanin kimiyyar siyasa a jami’an Abuja Dr. Abubakar Umar Kari ya yi bayanin cewa duba da abin da ya faru na tashe-tashen hankula musamman a jihohin Bauchi da Kano to ba makawa akwai hujjar yin fargabar barazanar tsaro yayin zaben.
Dr. Kari yace akwai bukatar jami’an tsaro suyi da gaske don kar da karshen wannan fargaba ta wakana, kuma ‘yan siyasa su daina daukar zabe a matsayin ko a mutu ko ayi rai.
A bangaren jami’an tsaro kuwa, hedkwatar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta shirya tsaf don tabbatar da tsaro a lokacin zaben.
CSP Almustapha Sani na sashen hulda da Jama’a a hedkwatar ‘yan sandan kasar ya ce an kara tura jami’an ‘yan sanda zuwa jihohin da za a gudanar da zaben da kuma sa idon manyan kwamishinonin ‘yan sanda.
Koda baya ga matakan na jami’an tsaro, a ce war masanin siyasa Dr. Sa’id Ahmed Dukawa na jami’an Bayero, adalci shine babban abin da zai tabbatar da zaman lafiya yayin zaben da ma bayan sa.
Dr. Dukawa ya ce a tabbatar da bin ka’ida kana duk wanda ya ci a bashi ba tare da magudi ba, muddin aka yi haka to duk wanda ya yi nasara za a mai biyayya, amma rashin bin hakan tabbas zai kai ga tashin hankali.
Hukumar wayar da kan Jama’a ta Najeriya wato NOA, ta jima tana ta yada sakon neman zaman lafiya a lokacin zaben kamar yadda shugabanta Dr. Garba Abari ke cewa muddin ba zaman lafiya to kome ka iya tabarbarewa.
Saurari cikakken rahoto daga Hassan Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5