Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Neja: PDP Ta Kalubalanci INEC Kan Matakan Tsaro Ranar Zaben Gwamnoni


'Yan Sanda A Jihar Zamfara
'Yan Sanda A Jihar Zamfara

Shugaban Jam'iyyar a Jihar ya bukaci hukumar zabe INEC ta tanadar da tsaro a lokacin zabe.

Tun farko dai jam'iyyar PDP ta yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasan da aka gudanar a jihar Neja, ranar 25 ga watan Fabrairun da ya gabata.

A wani taron manema labarai da Shugaban jam'iyyar ta PDP a jihar Nejan Barista Tanko Beji ya yi kira ga al'umma da su fito su yi zaben sannan ya bukaci hukumar ta INEC ta tabbatar ta yi tanadin jami'an tsaro a dukkanin rumfunan zabe dake fadin jihar Neja.

Jam'iyyar APC da ta nuna gamsuwa da yadda zaben ya gudana a baya amma tace rashin yawon takardun kudi a hannun jama'a ya kawo nakasu sosai a cewar shugaban APC a jihar Nejan Hon.Halliru Zakari jikantoro.

Hukumar zaben dai ta ce tana nan akan bakanta na tabbatar da yi wa kowa adalci a zaben kamar yadda Kwamishinan Hukumar zaben mai kula da Jihar Nejan Alh.Yusha'u Garki ya fada.

A yanzu dai hankali ya karkata zuwa ranar Asabar Mai zuwa yayin da masu ruwa da tsaki ke ci gaba da fadakarwa akan muhimmancin yin zaben lafiya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG