NIAMEY, NIGER - Tawagar manzonnin da kungiyar kasashen Afrika ta Yamma wato CEDEAO ta tura Jamhuriyar Nijar domin duba hanyoyin sulhunta bangarorin da ke takun saka a rikicin siyasar da ya samo asali daga juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023 ta koma Najeriya ba tare da samun wata amsa mai gamsarwa ba.
Yayin da a na su bangare sojojin da suka hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum suka ayyana rashin gamsuwa da huldar ayyukan soja a tsakanin Nijar da Faransa.
Tawagar wacce ta kunshi tsohon Shugaban Najeriya Janar Abdulsalam Abubakar da Sarkin Musulmi Mai Martaba Sultan Sa’ad na uku, ta sauka a filin jirgin saman Diori Hamani na Yamai da goshin magaribar ranar Alhamis 3 ga watan Agusta inda suka sami tarba daga Janar Moussa Salao Barmou.
Sai dai bayan zaman sa’oi a wani dakin taro da ke filin jirgin, wadanan manzonni sun juya zuwa Abuja da misalin karfe daya na dare ba tare da sun shiga birnin Yamai ba, ballantana su gana da jagoran Majalissar soja ta CNSP Janar Abdourahamane Tchiani, ko kuma da hambararen Shugaban kasa Mohamed Bazoum.
Shugaba Kungiyar CODDAE Moustapha Kadi na da kwarin gwiwa akan cewa Janar Abdulsalam Abukabar na iya samar da masalaha a dambarwar da ta barke bayan juyin mulkin na 26 ga watahn Yuli ganin rawar da ya taka wajen warware rikicin siyasar da aka yi fama da shi a Nijar a tsakanin shekarar 2009 zuwa 2010 lokacin tazarcen marigayi Tanja Mamadou.
A wata sanarwar da suka bayar, sojojin juyin mulkin sun ayyana rashin gamsuwa da yarjejeniyoyin ayyukan tsaro a tsakanin Nijar da Faransa, matakin da ke zama tamkar na share fagen kawo karshen huldar kasashen biyu a wannan fanni, inda Abdourahaman Alkassoum na ganin abin tamkar faduwa ce da ta zo dai-dai da zama.
Cikin salon irin na gugar zana, Majalisar ta CNSP ta yi barazanar kai hari wa daya daga cikin kasashen CEDEAO, ko da yake, ba ta bayyana sunan kasar da ta ke hangen afkawa ba wanda ke zama wata niyyar fadada yakin zuwa kasashe makwabta, muddin kasashen Yammaci suka zartar da kudirinsu na korar Janar Tchani da karfin soja.
Gwamanatin mulkin sojan ta sallami wasu jakadun kasar da suka hada da wanda ke Amurka da Faransa, na Najeriya da na Togo yayin da hambararen Shugaban kasa Mohamed Bazoum a makalar da ya aike wa Gwamnatin Amurka wacce aka wallafa a jaridar Washington Post ya bukaci ta taimaka ya koma kan kujerarsa kasancewarsa wanda ‘yan Nijar suka zaba a 2021 a matsayin Shugaban kasa na dimokradiya.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5