ABUJA, NIGERIA - Da sanyin safiyar ranar Alhamis 14 ga watan Satumbar ne 'yan Najeriya suka fuskanci daukewar wutan lantarki biyo bayan lalacewar da injin mai samar da wutan kasar ya yi gaba daya kamar yadda kamfanonin rarraba wuta da dama a cikin kasar suka tabbatar.
Lalacewar layin rarraba wutar dai ya jawo asara ga kayayyakin dake amfani da wuta a gidaje da masana’antu da kananan kamfanoni.
Sai dai bayan sa'o'i kadan da aka fuskanci wannan matsalar rashin wuta na gama gari, kamfanonin rarraba wutar lantarki a Najeriya kamar na Eko, Inugu da dai sauransu sun sanar da dawo da wutar daga layin dake rarrabawa ga dukkan sassan kasar.
Tuni dai ‘yan Najeriya daga sassa daban daban na kasar suka fara tofa albarkacin bakinsu a kan matakan da ya kamata gwamnatin kasar ta dauka don kawo karshen matsalar rugujewar tsarin samar da wutan lantarki ga al’ummarta.
'Yan Najeriya sun dade suna kira ga gwamnati ta sami tsayayyen mutum da zai rika kula da tsarin samar da ingantaccen wutan lantarki ne a kasar. Yayinda suka ce ya kamata gwamnati ta kara saka jari a cikn tsarin samar da wutan lantarki na hasken rana wato Solar don rage wa ‘yan kasar zafi.
A nasa bangare, kwararre a fannin makamashi kuma malami a jami’ar Sarki Fahad dake kasar Saudiyya, Dr. Yakubu Sani Wudil, ya bayyana cewa mafita ga matsalar katsewar aikin babban injin na samar da wutan lantarki a Najeriya sun hada da zuba kudi a fannin kayayyakin aiki, sannan a karkatar da akalar samar da wutan lantarki zuwa ga fannin hasken rana, iska, ruwa, sai kuma rage matsalar cin hanci da rashawa a fannin wutan lantarki.
Kamfanin kula da tsarin rarrabawa wutar lantarki na Najeriya wato TCN ya tabbatar da cewa katsewar hanyar wutan ya faru ne bayan wata gobara da ta tashi a layin Kanji/Jebba mai karfin 330kV 2, sai dai tuni masu ruwa da tsaki suka kaddamar da bincike a kan musababbin lamarin da nufin dakile afkuwar hakan nan gaba da kuma kara inganta aikin samar da wutar lantarki a kasar.
Alkaluman kididdiga daga kamfanin TCN, Najeriya na nuni da cewa, kasar ta fuskanci lalacewar babban hanyar samar da wutan lantarki a kasar akalla sau 46 tsakanin shekarar 2017 zuwa 2023, kuma a shekarar 2017 kawai an fuskanci katsewar wutar sau 15 wanda shi ne mafi yawa da aka taba gani a cikin shekarun baya-bayan nan.
Saurari cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5