Jagoran 'Yan Hamayya Hama Amadou Ya Koma Gida Nijar

Hama Amadou

Tsohon Firai Ministan Nijar Hama Amadou da ke hijira a kasashen waje ya koma gida da nufin bada gudunmowa a kokarin fitar da kasar daga dambarwar siyasar da ta biyo bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.

A yayin da magoya bayansa ke cewa zai taimaka a shawo kan takun sakar da ke tsakanin kasar da kungiyar ECOWAS wasu kuwa sun bukaci madugun ‘yan hamayyar ya kai kansa mashara’anta saboda laifukan da ake zargin ya aikata a baya.

A tsakiyar daren Litinin 11 ga watan Satumba zuwa wayewar Talata 12 ne Hama Amadou ya sauka a filin jirgin saman Diori Hamani na birnin Yamai bayan da ya shafe shekaru biyu a tsakanin Faransa da sauran kasashen duniya cikin wani yanayin da ke kama da gudun hijira mai nasaba da matsalolin da ya fuskanta a lokacin shudaddiyar gwamnati.

Kawo yanzu dai Hama Amadou bai fara bayyana a bainar jama’a ba lamarin da wasu na hannun damansa suka alakanta da maganar bin ka’ida.

Dawowarsa gida Nijar a wani lokacin da kasar ke fama da rikicin siyasa abu ne da wani kusa a jam’iyarsa ta Moden Lumana, Mahamadou Maidouka ke ganin zai taimaka a samo mafitar rikicin da ake fama da shi.

A jajibirin dawowarsa Nijar tsohon Firai Minstan a hirarsa da wata jaridar Faransa ya bayyana rashin jin dadi kan matsayin da Faransa da kungiyar CEDEAO suka dauka game da juyin mulkin da aka yi a wannan kasa musamman kan shirinsu na tursasa wa sojojin juyin mulkin da karfin bindiga, abinda wasu ke dauka tamkar gaisuwa ce da irin wake, sai dai magoya bayansa na cewa magana ce ta son kasa.

Abin tuni shine tsohon Firai Ministan na kulle a kurkukun Filingue a lokacin da ya sami izini daga wata kotun birnin Yamai a watan Afrilun 2021 don tafiya Faransa da nufin ganin likitinsa, sai dai kuma bayan shudewar wa’adin makwanni biyu da aka ba shi bai sake dawo wa Nijar ba. Wannan ya sa wasu ‘yan kasa ke fatan ganin tun da madugun ‘yan adawar ya dawo gida to ya kai kansa hannun hukuma don sauke nauyin da ke wuyansa a hukunce. Shugaban kungiyar Kulawa da Rayuwa Hamidou Sidi Fody na da irin wannan ra’ayi.

A taron manema labaran da ya kira a ranar 4 ga watan Satumba Firai Ministan gwamnatin rikon kwarya Lamine Zeine da ke amsa tambaya kan makomar fursinonin siyasa irinsu Hama Amadou, ya ce a shirye su ke su yi aiki da duk wani wanda zai bada gudummowa a ayyukan ci gaban kasa, abinda ake ganin ya kara wa tsohon Firai Ministan kwarin gwiwar dawo wa gida daga inda yake hijira.

Kakakin Majalissar Dokokin kasa Hama Amadou wanda a shekarar 2013 Gwamnatin Shugaba Issouhou ta zarge shi da laifin sayen jarirai ya arce daga Nijar ne a watan Agustan 2014 jim kadan bayan da kwamitin jagorancin Majalissar ya cire masa rigar kariya a wani shirin gurfanar da shi a gaban kotu.

Bayan dawowarsa gida a shekarar 2016 da 2020 madugun ‘yan hamayyar ya bakunci kurkuku a washe garin zaben 2021 saboda zarginsa da yunkurin tada zaune tsaye.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Jagoran 'Yan Hamayya Hama Amadou Ya Koma Gida Nijar.mp3