Iyayen Daliban Da Gobara Ta Halaka A Yamai Bara Sun Maka Hukumomi Kotu

Kungiyar lauyoyi matasa a Jamhuriyar Nijar da ake kira AJAN a takaice ta maka hukumomin kasar a kotu sakamakon rashin ganin wasu alamun biyan diyya ga iyayen dalibai kimanin 20 da gobara ta hallaka a birnin Yamai a watan Afrilun bara.

Watanni a kalla 9 bayan iftila’in da ya afkawa makarantar firaimarin unguwar Pays Bas dake birnin Yamai, har yanzu iyayen yaran da suka rasu sanadiyar wannan gobara na jiran jin wani abu daga wajen hukumomi game da batun biyansu diyya lamarin da ya sa suke ganin alamar nuna halin ko in kula akan wannan batu da ya jefa dimbin iyalai cikin halin damuwa.

Ta hanyar wannan kara iyayen yaran da suka rasu suna zargin hukumomin birnin Yamai da gwamnatin Nijar da hannu a faruwar wannan al’amari sakamakon rashin mutunta ka’idodin kafa makaranta da na tsarin gina azuzuwan karatu.

Muryar Amurka ta nemi jin matsayin hukumominilimi akan wannan batu amma haka ba ta cimma ruwa ba, yayinda bayanai ke nunin yiyuwar kotu ta fara zaman sauraren bangororin dake wannan fafatawa a ranar 2 ga watan Fabrairu dake tafe.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Iyayen Daliban Da Gobara Ta Halaka A Yamai A Bara Sun Maka Hukumomi A Kotu