Gbagbo Yace Bai Yarda Da Kara Sojojin Majalisar Dinkin Duniya A Ivory Cost

Shugaba Laurent Gbagbo na Ivory Coast.

Shugaban Laurent Gbagbo ya bayyana rashin amincewarsa da kiran da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na kara sojojin kiyaye zaman lafiya cikin kasar.

Shugaban Laurent Gbagbo ya bayyana rashin amincewarsa da kiran da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na kara sojojin kiyaye zaman lafiya cikin kasar.

Da yake magana Alhamis din nan,Gbagbo yace mai makon a kara sauran sojon baki daya su bar kasar,domin suna keta sharadin kasancewa ‘yan ba ruwana a harkokin siyasar kasar.

Majalisar Dinkin Duniya tace zata bukaci sojoji dubu daya zuwa dubu biyu a Ivory Coast,a lokacinda ake ci gaba da rikicin siyasa,yayinda shugaba Laurent Gbagbo ya dake ba zai mika mulki ba.

Ministan harkokin waje karkashin Gbagbo,Alcide Djedje yace rundunar majalisar dinkin duniyar mai karfin sojoji dubu 10, farar hula da ma gwamnatin Gbagbo basa kallonsu da sauran mutunci.

Djedje yace Majalisar Dinkin Duniya tana shishshigi cikin harkokin cikin gidan Ivory Coast,kuma tana hada baki da ‘yan tawaye.

Ahalin yanzu shugaban kasar mai jiran gado Alassane Ouattara,Alhamis ya zargi,Gbagbo da ruruta tarzomar da ta biyo bayan zaben,tareda baiwa wasu sojojin haya daga ketare umurnin kashe magoya bayansa.

Bangaren Gbagbo bai maida martani kan wan nan zargi ba.

A cikin wani sabon rahoto da ta gabatar,Majalisar Dinkin Duniya tace adadin mutane da tarzomar da ta biyo bayan zabe ta rutsa dasu ya kai 210.