Obasano Ya Kai Ziyarar Shiga Tsakani Ivory Coast

Wani yaro yake sussuka shinkafa a wani kauye a Ivory Coast.

Tsohon shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo, ya kai ziyarar neman shiga tsakani a rikicin kasar Ivory Coast jiya lahadi.

Tsohon shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo, ya kai ziyarar neman shiga tsakani a rikicin kasar Ivory Coast jiya lahadi.

Rahotanni na cewa wannan wani sabon yunkuri ne na Obasanjo na neman kawo karshen rikicin ta hanyar lumana.Olusegun Obasanjo ya sami tattaunawa da shugaba Laurent Gbago da kuma abokin jayayyarsa Alassane Ouattara.

Al’ummar kasa da kasa dai sun amincewa Alassane Ouattara ne sabon shugaban kasar Ivory Coast ganin cewa shine ya sami nasara a zaben shugaban kasa zagaye na biyun da aka gudanar a watan Nuwamban shekatrar data gabata, amma Laurent Gbagbo ya nace cewar shine ya lashe zaben don haka shi ba zai mikawa kowa ragamar mulki ba.

Kungiyar Cinikayya da inganta hulda a tsakanin kasashen Afirka ta yamma (ECOWAS) tayi barazanar amfani da karfin soja domin kauda Laurent Gbagbo,sai fa idan ya aminceya mika mulki ga wanda ya sami nasarar zaben Alassane Ouattara.