Isra’ila Ta Umarci Dakarunta Su Zauna Cikin Shirin Don Shiga Cikin Lebanon

Dakarun Isra'ila

Kalaman Babban hafsan sojin na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da kungiyar Hezbullah ta harba makami mai linzami kan hedkwatar hukumar leken asirin Isira’ila ta Mossad da ke kusa da Tel Aviv.

Babban hafsan sojin Isra’ila ya shaida wa dakarun kasar a ranar Laraba cewa su zauna cikin shiri domin kai farmaki ta kasa kan Lebanon.

Umarnin na zuwa ne a daidai lokacin da jiragen yakin Isra’ila suka yi lugudan wuta a kan mayakan Hezbullah a rana ta uku a jere.

Muna kai hare-hare ne a daukacin yini, domin sharar fage na yiwuwar shigarku, da kuma ci gaba da kai farmaki kan kungiyar Hezullah,” Laftanar Janar herzi Halevi, ya shaida wa wata rundunar tanka, a cewa wata sanarwar da sojojin suka itar.

Halevi ya ce “Ba za mu daina ba, Za mu ci gaba da kai musu hari da kassara su a ko’ina.” “Domin cimma hakan, muna shirye-shiryen kutsawa, kuma ma’anar hakan shi ne, takalmanku na sojoji, za su shiga yankin abokan gaba.”

Babban hafsan sojin ya yi magana da dakarunsa sa’o’i kadan bayan da kungiyar Hezbullah ta harba makami mai linzami kan hedkwatar hukumar leken asirin Isira’ila ta Mossad da ke kusa da Tel Aviv.