A yau Talata, Shugaban Amurka Joe Biden ya bukaci shugabannin duniya su kare kasar Lebanon daga afkawa cikin yaki, yayin da rikici ke kara kazancewa tsakanin Isra’ila da kungiyar Hizbullahi, abinda ya sanya babban sakataren majalisar dinkin duniya yin gargadi game da halin da ake ciki na, “daf da afkawa cikin yaki.”
Taron kolin Majalisar Dinkin Duniyar, wanda shine matakin karshe a tsarin diflomasiya, na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin Lebanon suka bayyana cewar hare-haren da Isra’ila ke kaiwa sun hallaka mutane 560 daga cikinsu yara kanana.
A jawabinsa na ban kwana ga Majalisar Dinkin Duniyar, Shugaba Biden yace, “babu wanda yake kaunar barkewar yaki. duk da cewar halin da ake ciki ya kazanta, amma har yanzu akwai damar warware rikicin ta hanyar diflomasiya.”
“Hakika hanya daya tilo ta samun tsaro mai dorewa ita ce ta kyale mazauna kasashen 2 su koma gidajensu dake kan iyaka cikin lumana,” a cewar biden.
Biden ya kuma yi tsokaci akan samun tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da kungiyar abinda ya ci tura, inda ya shaidawa Majalisar Dinkin Duniyar cewar har yanzu tana da sauran lokaci na “kawo karshen yakin.”
Biden ya kara da cewar yakin Shugaba Putin na Rasha ya gaza cimma babbar manufar da tasa aka kaddamar da shi. Manufarsa ita ce rusa Ukraine, amma har yanzu tana nan cikin ‘yanci.”
Babu tabbas ko taron kolin diflomasiyar zai iya cimma wani abun a zo a gani ga miliyoyin mutanen dake cikin yake-yake da fatara da rikicin sauyin yanayi a fadin duniya.
Dandalin Mu Tattauna