Isra’ila Ta Shiga Tsaka Mai Wuya Kan Kai Wa Hezbolla Harin Martani

Sojojin Isra'ila sun fafata da mayakan Hezbollah

Isra'ila ta ce tana son ta dauki fansa kan harin da Hezbollah ta kai mata, sai dai ta ce ba ta son ta jefa Gabas ta Tsakiya cikin yaki tsundum, kamar yadda wasu jami'an Isra'ila biyu suka fada a ranar Litinin.

Hakan na zuwa ne yayin da kasar Lebanon ta nuna kwarin gwiwa don mayar da martani bayan wani harin roka da ya kashe yara da matasa 12 a Tuddan Golan da Isra'ila ta mamaye.

Wasu 'yan Duze suna kukan rashin 'dan uwansu lokacin jana'iza a kauyen Majdal Shams wanda ke Golan Heights karkashin Isra'ila, Yuli 28, 2024.

Wasu jami'an Isra'ila biyu dai sun ce Isra'ila na shirye-shiryen yiyuwar fafatawa na 'yan kwanaki bayan harin roka da aka kai ranar Asabar a filin wasanni da ke kauyen Druze.

Dukkanin jami'ai hudu da suka hada da wani babban jami'in tsaro da kuma wata majiyar diflomasiyya, sun yi magana bisa sharadin sakaya sunansu, kuma ba su bayar da wani karin bayani kan shirin na Isra'ila na daukar fansa ba.

Manyan Druze lokacin jana'izar mutane 10 cikin 12 da rokar Lebanon ta kashe a Majdal Shams na Golan Heights, July 28, 2024.

Da yammacin jiya Lahadi, majalisar ministocin tsaron Isra'ila ta baiwa firaminista Benjamin Netanyahu da ministan tsaro Yoav Gallant izinin yanke shawara kan "hanyar da kuma lokacin” da za a mayar da martani kan harin makamin roka.

-Reuters