Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Isra'ila Kan Lebanon Ya Kashe Mutane 16 A Ci Gaba Da Tashin Hankali Kan Iyakokin Kasar


Lebanon-Israel
Lebanon-Israel

Wasu jerin hare-hare da jiragen yakin Isra'ila suka kai kudancin Lebanon sun kashe mutane 16, yayin da wasu rokoki da kungiyar Hezbollah ta harba ta yi sanadiyyar mutuwar wani Ba'isra'ile daya, wanda ya zamar da ranar Laraba nan mafi muni cikin sama da watanni biyar na gwabza fada a kan iyakar kasar

WASHINGTON, D. C. - Tun bayan barkewar yakin Isra'ila da Hamas a Gaza, ana kara nuna damuwa game da kara ruruwar tashin hankali a kan iyakar Isra'ila da Lebanon. Dubun duban mutane daga bangarorin biyu da rikicin ya rutsa da su sun rasa matsuguni.

Lebanon
Lebanon

Harin na Isra'ila na ranar Laraba ya shafi wata kungiyar siyasa da 'yan ta'adda ta 'yan Sunni ta Lebanon, kungiyar Islamic Group, wacce ta bi sahun kungiyar Hizbullah ta Shi'a a yakin da take yi da Isra'ila.

An kuma kashe mayakan Hezbollah biyu, da kuma wani kwamandan yankin na Amal Movement, wata kungiyar ta Shi'a.

Harin na farko da Isra'ila ta kai ta sama ya afkawa cibiyar kula da lafiya da ke da alaka da kungiyar Islama, inda ya kashe mambobinta bakwai a kauyen Hebbariye bayan tsakar dare.

Israel-Lebanon
Israel-Lebanon

Isra'ila ta ce ta kashe wani dan kungiyar Islama da ke da hannu wajen kai hare-hare kan Isra'ila, da kuma wasu mayaka da dama

Manjo Janar Ori Gordin, shugaban rundunar sojin Isra'ila a arewacin kasar, ya ce Isra'ila na kai farmaki kan kungiyar Islama, kuma ta kai harin "masu yawan gaske" kuma tana kai hare-hare masu yawa a kan Hezbollah

“Muna cikin yaki. Kusan rabin shekara kenan muna yaki, kuma ba zai kare da kungiyar Hizbullah ba,” kamar yadda ya shaida wa taron kwamandojin.

Kiryat Shmona an anrewacin Israel kusa da iyakar Lebanon Maris 27, 2024.
Kiryat Shmona an anrewacin Israel kusa da iyakar Lebanon Maris 27, 2024.

Sa'o'i kadan bayan harin ta sama, kungiyar Hizbullah ta dauki alhakin harba makaman roka a garin Kiryat Shmona da ke arewacin Isra'ila da kuma wani sansanin soji.

Hezbollah ta ce tana ramuwar gayya ne kan harin da aka kai cibiyar kula da lafiya.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG