Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Kokarin Kawar Da Barkewar Fada Tsakanin Hezbollah Da Isra'ila


Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe Biden

Jami'an Amurka sun ce suna aiki ta hanyar diflomasiyya don ganin an kawar da barkewar mummunan fada tsakanin Isra'ila da mayakan Hezbollah masu samun goyon bayan Iran da ke kudancin Lebanon.

Harin roka da aka kai daga cikin Iran biyo bayan tashin hankali tsakanin Hezbollah da Isra'ila
Harin roka da aka kai daga cikin Iran biyo bayan tashin hankali tsakanin Hezbollah da Isra'ila

Barazanar fadadar yakin a kan iyakar Isra'ila daga arewa na daga cikin bayanan da aka tattauna akai a jiya Alhamis a Washington, inda sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da mai bada shawara kan harkokin tsaron kasa a fadar White House Jake Sullivan suka gana da mai bada shawara kan harkokin tsaro na Isra’ila Tzachi Hanegbi, da Ministan kula da tsare tsare Ron Dermer.

Tattaunawar tasu ta kuma tabo batutuwa kan kokarin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin Gaza, da tabbatar da sako dukkan sauran mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su, da kuma kara kai agaji ga Falasdinawa farar hula.

Wani Sojan Isra'ila a bakin aiki
Wani Sojan Isra'ila a bakin aiki

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller ya fada wa manema labarai yayin wani taro a Isra'ila da Hezbollah, kawancen Hamas cewa, "Mun damu matuka game da halin da ake ciki a arewacin Isra'ila. Mun ga kungiyar Hezboallah tana kara kai hare hare kan kauyukan Isra'ila da wuraren jin dadin fararen hula, sabili da haka mu ke daukar matan diflomasiya na ganin lamarin bai ta'azzara ba."

Bangarorin biyu sun yi musayar wuta tun a watan Oktoba, lokacin da yakin Gaza ya barke.

A cikin watanni 8, an kashe fiye da mutane 400 a Lebanon, akasarinsu mayakan Hizbullah, amma kuma akalla fararen hula 80. A Isra'ila, an kashe sojoji 16 da fararen hula 11 a fadan.jiya Alhamis.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG