Ire-iren Azabar Da Mahukunta Suka Ganawa Al-Mustapha

Maj. Hamza Al-Mustapha leaves the court after a verdict in Lagos, Nigeria, on Monday, Jan. 30, 2012.

Manjo Hamza Al-Mustapha ya ambaci kadan irin ire-iren azabar da mahukunta suka gana masa yayin da yake tsare har na rsawon shekaru goma sha hudu.
Bayan ya kwashe shekaru goma sha hudu yana tsare a kurkuku shi da Alhaji Lateef Shofolahan, Manjo Hamza Al-Mustapha ya isa filin saukar jiragen sama ta Aminu Kano, Kano inda dubun dubatan jama'a suka fito kwansu da kwarkwatansu su tarbeshi.

Yayin da yake zantawa da wakilin Muryar Amurka Ladan Ibrahim Ayawa ya tabo abubuwa da dan dama.Ya sake nanatawa cewa ya yafewa duk wadanda suke da hannu a tsarewar da aka yi masa. Ya ce yana jin ba'a taba yiwa wani irin abun da aka yi masa ba. An bata masa lokaci a Legas na shekaru goma sha hudu. Ya ce ya ga alkalai kala-kala, wato alkalai daban daban. Ya ga alkalan magistiret biyu da kuma manyan alkalai goma sha biyu inda aka dinga juya shi daga wannan alkali zuwa wancan duk a kokarin hukuntashi. Ya ce an shirya makirce-makirce daban- daban har ma da wani da aka shirya a shekarar 2001 inda aka nemi a yi masu sharia cikin gaggawa a kuma kashesu a shekarar. To amma Allah da ikonsa wani da ya san cewa abun da ake fada a kansu ba daiadai ba ne sai ya bashi wannan takardar makircin da aka shirya. Ya ce lokacin da suka saka wannan takardar sai abun ya tsoratar da su. Kotun ta san cewa sun san makircin da gwamnatin dake Abuja ta lokacin da ta Legas ta wannan lokacin ke shiryawa.

Manjo ya ce ana sharia a kotu daban ana kuma wata sharia a shafin jaridu daban domin a bata masu suna. Duk wannan da nufin jama'a su nuna masu kiyyaya. Zamansu na tsawon shekaru goma sha hudu makaranta ce a wurinsu. Makaranta ce a wurin wadanda suka kulla masu makirci. Makarantace a wurin masu sharia. Mai shariar da ta sallamesu lokacin da ta karanta hukuncin karamar kotun kuka ta yi domin bata taba ganin irin wannan cin zaluncin ba duk rayuwarta har ta kai matsayin mai sharia a kotun daukaka kara.

Da farko da aka kama shi Manjo Hamza yace an daureshi. An ratayeshi. An kona shi da wuta cikin leda da sarka. An hana shi abinci. An kutuntawa iyalansa da kannensa. An kwashe duk abubuwansa. Wasu an konesu. Wasu kuma an kaisu wani wuri daban. Amma ya ce yau gashi idan Allah ya tashi kare maraya babu wanda ya isa ya hana. Shi da Manjo Hamza yana yiwa Allah godiya.

Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa.

Your browser doesn’t support HTML5

Ire-iren Azabar Da Mahukunta Suka Ganawa Al-Mustapha - 3.13