Da farko, mai shari’a tace karamar kotu ta nuna halin ko oho, na yadda babu wanda ya bayyana a kotu a cikin shaidu goma sha biyu domin bada shaida.
Ta ce hukuncin kisa, ba hukuncin wasa bane. Dole ne alkali ko kotu, ta tattara hujjoji masu nasaba da laifin wanda ake zargi da aikatawa, sabanin abinda karamar kotu ta yi.
Mai shari’ar ta kara da cewa an kasa kawo harsashin da aka ce da shi aka harbi Kudirat Abiola, domin a tantance shi a gaban kotu. Rita Pemu ta cigaba da cewa wani abun takaici shine yadda rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bari akayi amfani da ita a wannan shari’a, domin laifin kisa, yana bukatan binciken ‘yan sanda a matakin farko kafin a je Kotu.
A karshe mai shari’a Pemu tace, bisa hujjojin dake gabanta, hukuncin da karamar Kotu ta bayar, bashi da tasiri, bashi da karfi balle madogara, don haka, wannan kotu ba kowa take yi wa aiki ba, illa ‘yan Najeriya, kuma idan gaskiya ta fito, karya dole ta kauce. Akan haka, kotun daukaka kara ta sallami Manjo Hamza Al-Mustapha da Lateef Shofolahan.
Wannan shari’a an dade ana yinta. Shi dai Manjo Hamza Al-Mustapha, an tsare shi ne tun ranar 22 ga watan Oktoba 1998, akan laifuka da suka hada da kwashe kudaden marigayi Janar Sani Abacha, da yunkurin juyin mulki, da kuma kashe Hajiya Kudirat Abiola. Sannu ahankali, an sallami karrarakin banda na kashe Hajiya Kudirat, wanda sai yau aka kammala shari’arsa.
An kashe Kudirat Abiola ran 4 ga watan Yuni, shekara ta 1996.
A watan Junairun 2012 ne kotu a Ikkon ta yanke wa shi Mr. Al-Mustapha da Mr. Lateef Shofolahan hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Manjo Hamza Al-Mustapha shine shugaban masu tsaron marigayi tsohon Shugaban Najeriya wanda yayi mulkin soja, Janar Sani Abacha, kuma Al-Mustapha yayi shekaru 14 a tsare.