A cikin kalamunta ta cika da godiya ga Allah da duk wadanda suka tsaya da ita a tsawon shekaru goma sha hudu da mijinta ya yi yana tsare. Gidanta ya cika da mutane wadanda ta bayyanasu a matsayin masu tayata murna. Da aka tambayeta ko yaushe mijin nata zai iso ko kuma Abuja ko Kano zashi sai tace bata sani ba domin tana zaton akwai wasu ayyukan da masu zartaswa zasu yi kafin ya kama hanya.
Dangane da 'ya'yanta sai tace yaran da shekara da shekaru basu da uba har sun balaga amma sai gashi sun samu. Ta ce domin murna ma sai hawaye suke ta yi. Wata 'yarta ma da ba ita ba ce babba har ta gama jami'a dama digiri na biyu duk cikin lokacin da uban yana tsare.
Matar ta ce ba zata iya bayyana irin farin cikin da take da shi ba amma tana godiya ga Allah da jama' da suka dinga addu'o'i da kuma goyon bayan da suka bata.Ta ce ta godewa Allah da ya kawo wannan ranar farin ciki Ta kara da cewa duk abun da Allah ya bari ya samu mutum idan an tsare bangaskiya shi ya san yadda zai kawo sauki a lokacin da Ya ga ya dace.Ta godewa Allah da jama'ar duniya da suka taru suka rika yin addu'a suka kuma kasance tare da su duk tsawon lokacin wannan abun da ya samu mijinta. Ta yi addu'a Allah ya saka ma mutanen da suka tsaya dasu da alheri.Kawo yanzu dai bata samu ta yi magana da mijinta ba.
Ga rahoto da ya kara bayani.