Lateef Shofolahan, mutumin da aka saki bayan an wanke su da Majo Hamza al-Mustapha daga zargin kashe Kudirat Abiola, da aka yanke masu hukumcin kisa a kai, ya bayyana cewa, bai taba aiki a gidan marigayi MKO Abiola ba, bai kuma san dalilin da yasa aka kala mashi karyar da taja mashi daurin shekaru kusan 14 a gidan yari ba.
A cikin hirarsu da wakilinmu Ladan Ibrahim Ayawa bayan isarsu birnin Kano da Majo Al-Mustapha, Alhaji Shofolahan yace bashi da wata mu’amala da gidan marigayi ko wata hulda da marigayiya Kudirat da ta wuce bada dakuna ga kungiyoyin siyasa mata a otel din da aka bashi kula da shi lokacin kamfen din Abiola.
Ya kuma ce duk da yake bai san dalilin da yasa aka yi mashi wannan kagen ba, ya yafewa dukan wadanda ke da hannu a tuhumarshi.
Lateef Shofolahan ya yaba tare da bayyana godiya ga Majo Hamza Al-Mustapha sabili da kyakkyawan kulawa da iyalanshi bayan ya rasa dukan kaddarori da hanyar samun abin garnishi lokacin da yake gidan yari.