Rundunar sojan Amurka tace ba zata amince da duk yunkurin janyo cikas ga jigilar mai a mashigin ruwan Hormuz, bayan barazanar da Iran tayi cewa zata toshe hanayr ga jiragen ruwan dake dakon mai.
Wata mai magana da yawur rundunar sojan ruwan Amurka bataliya ta biyar dake Bahrain leftanar Rebecca Rebarich, ta gayawa Muriyar Amurka yau laraba cewa a shirye rundunar take ta tunkari duk wata barzanar da zata hana walwala da zirga zirga a wan nan mashigin, wacce tace tana da muhimmancin gaske ga tattalin arzikin yankin da ma Duniya bakin daya.
Tunda farko a wunin yau wani babban hafsa a rundunar sojan ruwan Iran Admiral Habibollah Sayyari yace toshe wana nan mashigin “abu ne mai sauki” ga rundunar sa,
Sai dai yace hukumomin Iran basu tsaida lokacin daukan wan nan mataki ba.