Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Paparoma ya shawarci Kirista cewa kar su mayar da hankali kan kele-kelen lokacin Kirsimeti kawai


Paparoma Bennedict
Paparoma Bennedict

A daidai lokacin da miliyoyin Kirista a fadin Duniya ke shirin

A daidai lokacin da miliyoyin Kirista a fadin Duniya ke shirin bikin Haihuwar Yesu Almasih, Paparoma Benedict ya yi Allah wadai da yadda aka mayar da lokutan Kirsimeti na kasuwanci.

A wani taron addu’a na jajabirin Kirsimeti a babbar Majami’ar St. Basilica da ta cinkushe da jama’a a jiya Asabar, Paparoman ya yi kira ga masubi da kar su mai da hankali kan kele-kelen wannan lokacin hutu amman su nazarci ainihin ma’anar wannan lokaci.

A halin da ake ciki kuma dubun dubatan masu ziyarar ibada su na ta isa birnin Baitalami tun daga jiya Asabar, don su yi Kirsimeti a garin da aka yi imanin cewa anan ne aka haifi Almasih.

Bukukuwan jajaberin Kirsimeti a wannan gari na yamma da kogin Jordan sun hada da sujada ta Mass ta tsakad dare a Majami’ar da aka gina a inda aka haifi Yesu wato Church of Nativity, inda Pastor Fuad Twal ya yi addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya musamman a gabas ta tsakiya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG