Babban jami’in diflomasiyar Iran, Abbas Araghchi, ya ja kunnen shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, a kan cewa a shirye Tehran take ta maida kwakkwaran martani da zai janyo nadama matukar Isra’ila ta kaiwa kasarsa hari a matsayin martani ga hare-haren makami mai linzami.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta harba kimanin makamai masu linzami 200 kan Isra’ila a ranar 1 ga watan Oktoba a matsayin ramuwar gayya kan kisan 2 daga cikin manyan makusantanta, shugaban kungiyar Hamas Isma’il Haniyeh da takwaransa na Hizbullah Hassan Nasrallah, dama wani babban janar din sojinta.
A makon daya gabata ne, Ministan Tsaron Isra’ila Yoav Gallant ya sha alwashin cewar matakin ramuwar gayyar da kasarsa zata mayar zai kasance “mummuna kuma wanda ba zai kuskure inda aka tura shi ba sannan mai ban mamaki.”
“A yayin da Iran ke yin duk mai yiyuwa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron yankin Gabas ta Tsakiya, a shirye take ta mayar da kwakkwaran martanin da zai haddasa nadama” akan dukkanin matakin da Isra’ila zata dauka, a cewar Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi yayin wata hira ta wayar tarho tsakaninsa da Guterres, inji sanarwar da ofishinsa ya fitar a yau Laraba.
A yayin hirar wayar tarho din data faru da yammacin ranar Talata, Araghchi ya kuma roki Majalisar Dinkin Duniya akan tayi amfani da dukkanin damar da take da shi wajen kawo karshen laifuffuka da cin zalin da gwamnatin Isra’ila ke aikatawa tare da aika kayan agaji zuwa Lebanon da Gaza”.