Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Ta Gano Gawar Wani Babban Kwamandan Dakarun Kasar Da Harin Isra’ila Ya Kashe Tare Da Hassan Nasrallah A Watan Satumba


Yayin addu'a ga marigayi Sayyed Hassan Nasrallah,a Tehran
Yayin addu'a ga marigayi Sayyed Hassan Nasrallah,a Tehran

A jiya Juma’a Iran tace, ta gano gawar wani janar din sojin juyin juya halin da aka kashe tare da jagoran Hezbollah Sayyadi Hassan Nasrallah a yayin wani harin da Izra’ila ta kai a watan jiya a Beirut.

Rundunar sojojin juyin juya halin ta fada a cikin wata sanarwa cewa, sakamakon namijin kokarin da akai tayi ba ji ba gani, a karshe an gano gawar shahidi Abbas Nilforushan.

Bangaren dakarun kasar ta Iran ya kara da cewa, a nan gaba ne za’a sanar da lokacin daukar gawar shahidi Nilforushan zuwa kasar shi ta musulunci, da shirye shiryen yi masa sutura

Nilforushan babban kwamandan dakarun kurdawa ne na IRGC, bangaren ayyukan ketare, da aka kashe a ranar 27 ga watan Satumba, tare da Sayyadi Nasrallah.

A ranar 1 ga watan Oktoba, dakarun juyin juya hali suka harba makamai masu linzami guda 200 zuwa cikin Isra’ila, a matsayin ramuwar gayya ga kisan janar din, da ma kisan Nasrallah da Isma’il Haniyeh, jagoran siyasa na kungiyar Hamas dake Gaza wadda Iran din ke marawa baya, wanda aka kashe a Tehran a karshen watan Yuli.

A makon nan mai karewa ne ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant yace martanin da kasar sa zata maida, zai kasance, mummunan martini da ba zai kuskure ba, da zai bada mamaki.

Kasar ta Parisa, wato Iran tayi alkawarin maida martini, muddin babbar makiyiyar ta Isra’ila, ta kai mata hari.

Da yake jawabi gaban kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Alhamis, wakilin Iran na din din din a majalisar dinkin duniya, Amir Saeid Iravani, yace, jamhuriyar musuluncin na shirye daram ta kare diyaucin kasar ta daga duk wani zalunci ko farmakin da za’a kai kan tsaro da muradun ta.

Yace, Iran ba ta neman yakin ya fadada, to amma zatayi amfani da ikon da take da shi wajen kare kan ta daidai da dokar duniya, za kuma ta sanar da kwamitin tsaro game da martanin da zata mayar bisa doka.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG