Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Macron Ya Caccaki Isira’ila Kan Farmakin Gaza Da Lebanon


Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron

Macron ya nanata damuwarsa kan rikicin Gaza da ke ci gaba, duk da kiran da ake ta yi na a tsagaita wuta.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi kira a ranar Asabar cewa, a dakatar da kai wa Isira’ila makamai domin yin amfani da su a Gaza, lamarin da ya harzuka firai ministan Isira’ila Benjamin Netanyahu ya mayar da martani mai zafi.

Ya kuma soki matakin da Netanyahu ya dauka na tura dakaru zuwa kai farmaki ta kasa a Lebanon.

Macron ya shaida wa kafar yada labaran Faransa ta France Inter cewa “Ina ganin cewa a yau, bababn abin da za mu sa a gaba shi ne mu koma amfani da mafitar siyasa, mu daina kai makaman yaki don yaki a Gaza.”

A wata hira da aka nada a ranar Talata, ya kara da cewa, “Faransa ba za ta sake kai komai ba.”

Macron ya nanata damuwarsa kan rikicin Gaza da ke ci gaba, duk da kiran da ake ta yi na a tsagaita wuta.

Jawabinasa ya janyo martani nan take daga Netanyahu.

Netanyahu ya fada a ciki wata sanarwa da ofishinsa ya fitar cewa, “Yayin da Isira’ila ke yaki da dakarun dabbanci da Iran ke jagoranta, ya kamata dukkan kasashe da ke da wayewa su tsaya tsayin daka wajen goyon bayan Isira’ila.”

“Amma duk da haka, Shugaba Macron da sauran shugabannin Yammacin Duniya suna kira da a kakabawa Isira’ila takunkumin makamai, abun kunya gare su.”

Sanarwar ta kara da cewa Isira’ila tana yaki da kungiyoyi da dama da ke samun goyon bayan babbar makiya Iran.

AFP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG