Yanzu haka dai majilisar dokokin kasar ta Amurka tana da sauran sati bakwai daga cikin kwanaki 60 da take dasu na amincewa da wannan yarjejeniyar ko kuma akasin hakan, wanda za ayi musayar sa cire mata takunkumin da aka sa mata.
Sai dai kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wadannan makonnin domin samar da lokaci na musammam wanda zaisa a cire wa kasar ta Iran wannan takunkumi zuwa karshen wannan shekarar.
Kerry shi da Moniz da kuma sakataren baitulmali Jacob Lew wadanda sau tari suka sha ganawa da jami'an kasar Iran domin samun daidaito na yarjejeniyar da aka cimma ana kokari a kai. A farko watan gobe zasu bayyana gaban kwamitin kula da harkokin kasashen waje na majilisar dattawan Amurka.
Ko a satin da ya shige wadannan mutanen ukku sun huskanci kwamitin inganta zumunci da kasashen ketare inda Kerry yace watsi da wannan yarjejeniyar wani fatali ne da damar data samu domin kawo karshen batun sarrafa makamin nukiliya na kasar Iran wanda zai anfani duniya baki daya