Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya bayyana cewa kuri’ar da kwamitin sulhun MDD ya jefa domin dage takunkumin da ya kafa ma kasar Iran, alama ce ta nuna yarda da yarjejeniyar da kasar ta cimma da wasu manyan kasashe 6 na duniya kan shirinta na nukiliya.
A cikin wata hirar da yayi da sashen Farisanci na VOA, Sakatare Kerry yace su kansu ‘yan kasar ta Iran zasu ci moriya idan har hukumominsu suka aiwatar da wannan yarjejeniya tsakani da Allah.
Sakataren Harkokin wajen na Amurka, yace "ina jin cewa idan har dukkan sassan suka zartas da wannan yarjejeniya, aka aiwatar da ita sosai, al’ummar kasar Iran zasu ga ingantuwar rayuwa, za a dage takunkumin da aka sanya ma kasar, harkokin tattalin arzikin kasar zai bunkasa saboda kasuwanci, tafiye-tafiye da makamantansu duk zasu karu."
Ita dai wannan yarjejeniya, ana bukatar sai majalisar dattijan Amurka ta amince da ita, amma kuma akwai matsala a saboda ‘yan Republican da dama a majalisar sun lashi takobin ganin cewa ba a yi hakan ba. Masu sukar lamirin wannan yarjejeniya, sun ce ba ta biya bukata ba, domin maganar nukiliya kawai ta yi, ba tare da sauran batutuwan da Amurka take takun saka da Iran a kai ba. Sakatare Kerry yace akwai dalil
Ya kara da cewa, "Muna iya kaiwa har shekaru goma cur muna tattaunawa idan da mun ce zamu tattaro batutuwan da kasar Iran take takaddama da su tsakaninta da sauran kasashen duniya ne ba tgare da mun cimma wani abu ba. Yanzu ma a kan batun nukiliyar kawai, shekaru 4 muka shafe muna tattaunawa da su."
Sakatare Kerry, yace wannan yarjejeniya ta nukiliya da kasar Iran, ta tarihi ce wadda kuma zata biya bukatar kowane bangare, watau su kasashen duniya zasu tabbatar cewa Iran ba ta kera makamin nukiliya ba, yayin da ita kuma za a janye takunkumin da ya nakkasa mata tattalin arziki.