Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Laraba Sakataren Tsaron Amurka Zai Kai Ziyara Saudiya


Sakataren Tsaron Amurka Ash Carter ya gana da Sarkin Saudiya Salman bin Abdul Aziz (R) a fadar Al-Salam dake Jeddah.
Sakataren Tsaron Amurka Ash Carter ya gana da Sarkin Saudiya Salman bin Abdul Aziz (R) a fadar Al-Salam dake Jeddah.

A cigaba da kokarin kwantar da hankalin kawayen Amurka dake adawa da yarjejeniyar da aka cimma da Iran akan shirin nukiliyarta, Ash Carter ya kai ziyara Saudiya.

A yau Laraba, Sakataren tsaron Amurka, Ash Carter zai kai ziyara kasar Saudi Arabia, a wani mataki na nemarwa matsayar da aka cimma kan batun nukiliyar Iran farin jini a tsakanin kawayen Amurka.

Hukumomin Saudiyya dai basu yi tur ko na’am da matsayar ba, wacce aka cimma a ranar 14 ga watan Yuli.

Ana sa rana Carter zai gana da Sarki Salman da ministan tsaron kasar kafin ya kama hanyarsa ta komawa Jordan, inda zai gana da shugabannin dakarun kasar.

A jiya Talata, Carter ya gana da dakarun hadin gwiwa a arewacin Jordan a wani sansanin Soji da ke daukan ragamar tsara yakin da ake yi a Syria.

Daga dai Isra’ila Catrer ya yada zango ne a Jordan inda ya gana da Firai Minista Benjamin Netanyahu, ziyarar da ya kai domin nuna ci gaban goyon bayan Amurka ga Isra’ila.

Rahotanni sun Mr Netanyahu bai saki fuska kamar yadda ya saba ba a lokacin da ya tarbi Carter.

XS
SM
MD
LG