Inter Miami Ta Taya Messi Murnar Lashe Ballon D’Or

Messi

A karshen watan da ya gabata aka karrama Messi da kyautar a birnin Paris na kasar Faransa.

Kungiyar Inter Miami a gasar kwallon kafar Amurka ta MLS, ta taya dan wasanta Lionel Messi murnar lashe kyautar Ballon D’Or.

Wannan shi ne karo na takwas da Messi yake lashe wannan kyauta a rayuwarsa ta kwallo.

An yi wasan wuta don taya Messi dan asalin Argentina murna gabanin wasan sada zumunci da aka shirya da kungiyar New York City FC a ranar Juma’a don taya shi murna.

A karshen watan da ya gabata aka karrama Messi da kyautar a birnin Paris na kasar Faransa.

An ga Messi ya dauki kofin a tsakiyar filin a hannunsa na hagu ya kuma daga shi sama yayin da jama’a suka barke da shewa.