Lionel Messi ya lashe lambar yabo ta Ballon d’Or a karo na takwas a Paris, babban birnin Faransa.
Dan wasan na Argentina ya jagoranci kasarsa wajen lashe kofin duniya a Qatar a shekarar da ta gabata.
Kofin na gasar cin kofin duniya shi ne kadai da ya ragewa Messi ya lashe a rayuwarsa ta kwallo.
Messi wanda yake taka leda a kungiyar Inter Miami a Amurka ya doke Erling Haaland na Manchester City wajen lashe kyautar ta Ballon d’Or a bana.
‘Yar wasan Sifaniya Aitana Bonmati ce ta lashe kyautar ta Ballon d’Or a bangaren mata bayan da ta jagoranci kasarta ta lashe kofin gasar cin kofin duniya ta mata a watan Agusta.
Kazalika ta taimakawa Barcelona lashe kofin gasar zakarun nahiyar turai ta mata.
Dandalin Mu Tattauna