Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lionel Messi Na Shirin Komawa Kungiyar Inter Miami Ta Amurka


FILE PHOTO: Lionel Messi
FILE PHOTO: Lionel Messi

Fitaccen dan wasan kwallon kafa Lionel Messi ya sanar da aniyarsa ta shiga kungiyar Inter Miami ta Amurka a matsayin dan wasa mai zaman kansa bayan ya rabu da kungiyarsa ta Paris Saint-Germain dake Faransa, kuma ya yi watsi da tayin kwangila mai tsoka a Saudi Arabiya.

Messi, wanda ya buga wasansa na karshe a PSG a karshen mako kuma ana alakanta shi da komawa Barcelona, amma babu gurbi a kungiyar ta Spaniya saboda ka’idar kudi ta La Liga.

Messi ya shaidawa jaridun Mundo Deportivo da Sport cewa yanzu yana dab da kammala yarjejeniya da Miami.

Magoya bayansa a kasarsa ta Argentina sun mayar da martani ga shirin Messi na komawa Miami. Inda mafi yawa ke cewa ganin irin jajircewarsa da kuma farin ciki da ya dade yana baiwa magoya bayansa, yanzu zai iya yin duk wani abu da yake so.

Messi ya ce idan bai sami komawa kungiyar Barcelona ba, to yana so ya bar Turai, ya fita daga idon shahara kuma ya kara tunani game da iyalinsa.

Messi ya so ya je kulob ne inda a karshe zai iya samun hannun jari, kamar yadda wata majiya da ke da masaniya kan tattaunawar ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a wannan makon.

Har ila yau, yana so ya habaka yarjejeniyar da kamfanin Adidas da hukumar MLS da kuma kamfanin fasaha na duniya, Apple.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG