Duk da cewa Lionel Messi ya buga wasan da Argentina ta doke Paraguay da ci 1-0 a makon da ya gabata, hakan ba ya nufin zai fara kara wa a wasansu da Peru a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.
Messi a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na AP, ya daure ya buga zango na biyu a wasansu da Paraguay duk da cewa yana fama da ciwon jijiya cikin makonnin da suka gabata.
Sai dai babu tabbacin zai buga wasa na gaba da Argentina za ta buga da Peru a ranar Talata.
A wani labarI kuma ana ta caccakar dan wasan Brazil Neymar, saboda zargin sa da rashin tabuka komai a wasan da Brazil ta tashi da 1-1 da Venezuela a makon da ya gabata.
Lamarin har ya kai ga magoya bayan Brazil suna watsa gurguru a filin wasa na Pantanal a Cuiaba.
Yanzu dai yana da babban kalubale a karawar da Brazil za ta yi da Uruguay, inda za a sa ran tauraruwarsa za ta haska.
Za a yi gasar cin kofin ta gaba a shekarar 2026 a Amurka, Canada da Mexico inda za a kara adadin kasashen da ke halartar gasar zuwa 48.
Dandalin Mu Tattauna