INEC Ta Hannunta Kwamishinan Zaben Jihar Adamawa Ga 'Yan Sanda

Shugaban hukumar zabe ta INEC Farfesa Yakubu Mahmood

Hukumar zaben Najeriya INEC ta mika batun binciken kwamishinan ta na zabe a jihar Adamawa Barista Ari Hudu ga babban sufeton ‘yan sanda Baba Usman Alkali don daukar matakin doka da ya dace.

ABUJA, NIGERIA - Hukumar ta INEC tun farko ta dakatar da kwamishinan zaben don samun sa da laifin ayyana sakamakon zabe ba tare da hurumin yin hakan ba.

INEC dai ta gana da dukkan masu ruwa da tsaki na lamarin zaben na jihar Adamawa don shirin sake komawa tattara sakamakon biyo bayan hatsaniyar da ta auku.

Magoya bayan ‘yar takarar APC Aisha Binani ke nuna gamsuwa ga ayyana su a matsayin wadanda su ka lashe zabe, yayin da bangaren gwamnan jihar Umar Fintiri na PDP ke cewa an yi mu su murdiya.

Jami’a a sashen labarun hukumar Zainab Aminu ta ce hukumar na daukar dukkan matakan da su ka dace bisa dokokin zabe don tabbatar da adalci.

Duk da gamsuwa da dakatar da kwamishina Hudu Ari, wakilin gwamna Fintiri a dakin tattara sakamako Dr. Idi Hong na bukatar daukar matakan shari’a kan kwamishinan.

Magoya bayan Binani a Abuja na musanta zargin ba da toshiyar baki ga jami’an zabe bisa wani faifan bidiyon tuhuma da ke yawo a yanar gizo.

Bara’atu Garba Yusuf na kan gaba a masu nuna Aisha Binani ba ta yi wani abu na taka doka ba.

Masanin harkokin siyasa na jami'ar Abuja Dr. Farouk B.B Farouk ya ce da alamun badakala na kara tagaiyara tsarin zabe a Najeriya.

Za a jira sake komawa fagen tattara sakamakon zabe da ya nuna karin sa ido da daukar matakan tsaro don kar a kwari kowa.

Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-Hikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

INEC Ta Mika Bincike Ga Sufeton ‘Yan Sanda Kan Kwamishinan Zabe Na Jihar Adamawa.mp3