Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Baza Jami’an Tsaro A Sassan Adamawa Yayin Da Ake Sake Zaben Gwamnan Jihar


Zaben jihar Adamawa
Zaben jihar Adamawa

An girke jami'an tsaro masu yawa yayin da jama’a suka nufi rumfunan zaɓe ranar Asabar don a kaɗa ƙuri'ar zaɓen gwamna a Yola babban birnin Jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Ranar Asabar 15 ga watan Afirilu ake gudanar da zaɓe a rumfunan zaɓe sittin da tara a faɗin jihar Adamawa don zaɓen gwamnan jihar, bayan da aka fafata a watan Maris amma zaben bai kammala ba.

Ƙorafe-korafe da suka biyo bayan zaɓen jihar ne suka sa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC ta ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba.

Zaben jihar Adamawa
Zaben jihar Adamawa

Da ƙarfe 8 na safe ya kamata a fara zaɓe a ƙauyen Ajiya da ke makwabtaka da Yola, amma an samu jinkiri yayin da gwamman mutane suka yi zaman jira har tsawon kusan awa ɗaya domin su kaɗa kuri'arsu.

Zaɓen da aka yi ranar 18 ga watan Maris ya zo cike da takaddama da zarge-zargen maguɗi, wanda duka manyan ‘yan takara biyu, gwamna mai ci na jam'iyyar PDP da ta jam'iyyar adawa ta APC suka yi wannan iƙirari.

Zaben jihar Adamawa
Zaben jihar Adamawa

A sakamakon zaɓen da INEC ta bayyana a baya, gwamna mai ci Ahmadu Umaru Fintiri ne ke kan gaba da ƙuri'u 421,524 yayin da Sanata Aishatu Dahiru Binani ke biye da kuri’u 390,275, lamarin da ya sa kuri'a 31,249 ce ke tsakanin 'yan takarar biyu.

Idan Aisha Binani ta yi nasara, za ta zama zaɓaɓɓiyar gwamna mace ta farko a Najeriya.

Salisu Lado.

XS
SM
MD
LG