INEC Ta Bukaci A Hukunta Kwamishinan Zaben Jihar Adamawa 

Shugaban hukumar zabe ta INEC Farfesa Yakubu Mahmood

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta bukaci babban sufeto janar na ‘yan sandan kasar Alkali Usman Baba daya gaggauta kama tare da gurfanar da dakatatten kwamishinan zaben jihar Adamawa Barista Hudu Yunusa Ari.

ABUJA, NIGERIA - INEC ta gudanar da wannan bukata ne akan zargin kwamishinan zabe na jihar Adamawa Barista Hudu Yunusa Ari da taka doka na yin azarbabin bayyana wanda ya ci zaben gwamna a jihar.

Hukumar ta INEC ta nemi wannan bukata ne cikin wata sanarwa bayan wani taron gaggawa da hukumar tayi kan batun danbarwar zaben na Adamawa.

“Tuni an rubutawa babban sufeto janar kan ya gaggauta bincika tare da garfunar da kwamishin zaben Adamawa Barista Hudu Yunusa Ari.”

Haka zalika INEC ta bukaci babban sakataren gwamnati da ya duba halinda kwamishinan ya nuna don daukar matakin da ya dace.

Mahmud Yakubu Shugaban INEC

Hukumar da bayyana cewa baturan zaben jihar ne yanzu yake da hurumin bada lokacin da za’a dawo da ci gaba da karbar sakamakon zaben.

Tuni dai hukumar ta INEC ta dakatar da Barista Hudu tare da gargadinsa daya guji zuwa kusa da ofishin hukumar.